Ganduje: Ashe Tusa Za Ta Hura Wuta Inji Dr Sherif Al Muhajjir

Babban marabucin harshen hausan nan wato Dr Sherif Al Mihajir bai ji dadin yadda gwamna ganduje ke tafiyar da lamarin mulkin shi ba. Dr sheriff ya hau kan yanar gizo yana kalubalantar sabuwar nadin mukamin da gwamna ganduje yayiwa yar fim wato Yuhanasu Sani.

Dr Sherif de ya dade yana rigima da yan wasan Kannywood, kuma baya boye ra’ayinshi nacewa wai yan kannywood suna kawo lalacewar tarbiya a arewacin najeriya.

ga dai abin da Dr ya rubuta:

Wannan gomnan na Kano yana bukatar chanza dukkan mashawartan shi, da ma duk wani amini da ke tare da shi.

Maganar gaskiya babu yadda zaa yi duk wani mai son shi ya bar shi ya Nada Yar drama matsayin mai ba shi shawara kan harkar Kasafin Kudi. Bayan ya Nada wata ma akan harkar mata kwanaki.

Ina tsammani ko da yana kaunar yan drama ya kamata ya gane cewa akwai ayyukan da ya dace da su. Ina gani ba zai zama karya ba idan nace wannan baiwar Allah ba ta taba ganin kunfin kasafin kudi ba, balle ta baka shawara akan shi ya kai PhD Ganduje.

A Kano, muna da irin su Barrister Huwaila Muhammad wadanda su ka bata lokaci dukiya da dukiya don su tafiya Bayelsa kokarin dawo da Martaba Arewa da masarautar Kano, bayan kun dauki mataki ba tare da bincike mai zurfi ba, amma duk sun zama shirme sai yan drama? Wannan wanne irin shugabanci ne?

Adawa daban shawara daban gaskiya wannan ba karamin kuskure ba ne daga gomnan gari mai tarin ma su ilimin tattalin arziki kamar Kano.

Ita kuma wannan mai mika appointment din ko wacece oho?

 

Ku so mu a shafinmu na facebook domin ku sami labari na kayatarwa akan lokaci:

www.facebook.com/knottedposthausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: