Bama cikin Rigimar Kwankwaso da Ganduje- Danbilki Commanda

A Najeriya wasu magoya bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Kano sun nesanta kansu daga rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.

Wasu masu lura da al’amura dai na ganin wannan rikici na iya shafar makomar jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kano, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke da dumbin magoya baya.

Malam Abdulmajid Danbilki Kwamanda, jigo ne a bangaren masu goyon bayan shugaba Muhammadu Buharin a jihar Kano, ya shidawa Knottedpost cewa ba ruwansu da rikicin su a matsayin ‘yan ba ruwanmu suke.

Ya kara da cewa rikici irin wannan babu abinda ya ke janyowa a jam’iyya face rarrabuwar kawuna.

Danbilki yace a yanzu su abinda suka sanya a gaba shi ne yaya za a kawo ci gaba ga al’umar Najeriya, da taimakawa shugaba Muhammadu Buhari sauke nauyin da yake kansa na amanar kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: