Kungiyar yan Kwangila tace tana da takaddu akan Kwankwaso

Hadadiyar Kungiyar yan kwangilar najeriya reshen jahar kano tace wai tana da takaddu akan tsohon gwamnan jahar kano, Dr Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban Kungiyar Auduwa Maitangaran shi ne ya shaidawa yan jarida, inda yace gwamnatin sanata kwankwaso ta bar bashi na sama naira bilyan dari biyu, kuma wai su yan kungiyar suna rubutatciyar shaidar  irin siddabarun da yan waccan gwamnatin sukayi.

Alhaji Maitangaran yacce wai tsohowar gwamnatin ta bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba kuma wai ta biya yan kwangilolin goge.

Alhaji Maitangaran yacce a shirye ita kungiyar takke tafito wa’ennan takardaun wai domin a biye wa yan kungiyar hakkinsu a wajen tsohuwar gwamnatin.

Wannan dai itace sabuwar barazanar da Kwankwasiyya takke fiskanta tun da aka samu baraka tsakanin tsohon gwamnan da gwamna Ganduje

Leave a Reply

%d bloggers like this: