Siyasar Kano- Gwamnonin Arewa sun nemi sulhunta Kwankwaso da Ganduje

Gwamnonin Jihohin Arewa musamman na Jami’iya mai jan ragamar gwamnati wato APC sun dauki alwashin sulhunta Kwankwaso da tsohon mataimakin sa Abdullahi Ganduje.

Rigima dai ta barke tsakanin Kwankwaso da Ganduje tun bayan da tsohon gwamnan ya zo kawo ziyarar gaisuwa ga Gwamna Gandjue dangane da rasuwar mahaifiyar sa. Ganduje ya zargi Kwankwaso da Zagin sa da zagin mahaifansa wai domin sabuwar gwamnatin bata chigaba da wa’ensu ayyukan da Kwankwaso ya fara ba.

Majiyarmu ta nemo cewa gwamnonin Jigawa, da Katsina da Sokoto do kebbi da zamfara tarre da wa’ensu yan majalisun Kano irin su Senata Kabiru Gaya da Alhaji doguwa sun zona da Ganduje a masaukin gwamnanatin Jihar Kano dake Abuja.

Majiyarmu tace koda shi Kwankwaso bai sami hallitar wannan taron ba, ya taofa yawun yarda, inda gwamnonin Arewan sukayi alkawarin cewa duk sulhun da suka zartar tau ya zauna.

Bayan gamuwar sa da shugaban kassa yau da zafe, Gwamna Ganduje ya nemi kawar da maganr rigimar inda yacce ai “Shi da kwankwaso yan uwa ne kuma Aminan juna ne” ya kara da cewa “rashin jituwa tana iya faruwa a cikin ko wanne irin abokantaka ko yar uwantakka kuma sulhu bazai taba gagaraba”

Jamiyar APC a jahar Kano karkashin Kwankwasiyya dai tayi nassarar Siyasar da ba’a taba samun irinta ba a tarihin Siyasar Kano, inda ta lashe dukkan kujeru dari bisa dari a dukkan zababbuka da akayi a jahar. Wannan rigima ta sa gwamnonin APC sun ja jinin jikinsu inda suke tsoran kada rigimar ta haifar da baraka a sauran Jahohi musamman gamme da la’akari da yaran da gwamna kwankwaso ya kafa a sauran Arewacin Najeriya.

Senata Shehu Sani na Kaduna da wasu magoya baya tuni sun bayyanawa jamma’a irin gudumuwar da kwankwaso ya basu a kaduna, inji su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: