Yahanasu ta zama Adviser, Yan fim na Shakatawa a gwamnatin Ganduje

Lalle gwamna ganduje ya zama babban abokin yan fim, dan tun da ake gwamnati a arewacin najeriya ba’a taba samun gwamnan da ya janyo yan fim ajiki ba.

A yunzu haka dai Yahanasu Sani ta zama yar fim ta uku wadda Ganduje ya bawa mukami a cikin gwamnatin sa

n2 n3

Tau komai ya janyo wannan sabon sallon da yan siyasa ke dauka a halin yunzu?

Tun dai da gwamnatin Mal Ibrahim Shekarau ta ragargaji su kuma ta kusan karya musu industry, yan fim sun daukin alwashin shiga siyasa domin su karre harkar cin abincinsu. Mafi yawansu sun gano cewa rayuwa lalle tafi dadi idan gwamnati najin tsoran daurre ka ko yi maka katsafi. wannan tasa da yawan su suka garjaya cikin siyasa.

Abun na biyu kuma, bayan rawar shari’a wadda su Yeriman Bakura da Shekarau suka tabka, yan siyasa dayawa sun ganno cewa lokacin ci da addinni lalle ya fara shigewa, hakan tasa mafiyawan yan siyassar ke kusantar yan fim domin ko zasu lashi barkar jamma’ar da Allah ya basu.

Ku so my shafinmu na Facebook domin ku sami labarai na aiwatarwa akan lokaci:

www.facebook.com/konttedposthausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: