Za’a Kafa Hisbah a Katsina- Masari

Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin shugabancin Gwamna Aminu Bello Masari za ta kafa kwamitin da zai yi nazari a kan dokar da ta kafa hukumar Hizbah ta jihar Kano domin duba yiwuwar kafa irin wannan hukuma a nan jihar ta Katsina. Gwamnan Jihar ta Katsina ne ya bayyana hakan a yayin da aka gabatar masi da kwafen kundin dokar daga hannun Babban Kwamanda kuma Shugaban hukumar Hizbah ta jihar Kano watau Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa a yayin wata ziyara da suka kawo a gidan Gwamnati.

Gwamnan Masari ya kara da cewa “kafawa tare da tabbatar da ana aiki da irin wadannan dokoki a makwabtan jihohi ne zai tabbatar da samun biyan bukata”.

Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana irin nasarorin da hukumar ta Hizbah ta samu a jihar Kano musamman wajen rage yawan bata gari da kuma manya da kananan laifuka. Ya kara da cewa sun kuma sami nasara kwarai wajen rage yawan shari’u da ake kaiwa kotuna ta hanyar yin sulhu tsakanin al’umma, sannan kuma da rage yawan barace barace a tituna da cikin unguwanni. Babban Kwamandan ya kara da cewa “mun shigo da tsare tsare da dama domin kyautata zamantakewar iyali, musamman wajen inganta hanyar neman Aure da kuma kyautata zaman rayuwar Auren. Ya kuma danganta wannan nasarori da suka samu ga irin cikakken goyon bayan da Gwamnatin jihar Kano take ba su, sannan kuma da shigo da Masarautar Kano da kuma duka kungiyoyin addini irin su Darika Izala da sauran su wajen gudanar da ayyukan hukumar”.

A karshe ya yi kira ga Gwamnatin jihar Katsina da ta yi koyi da ta Kano wajen kafa hukumar Hisbah domin hakan zai kawo maslaha kwarai a cikin tafiyar da rayuwar al’umma

Za’a kafa hukumar Hizbah a Jihar Katsina

Leave a Reply

%d bloggers like this: