El Rufai Makaryaci Ne Inji Shehu Sani

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani, yayi kira gay an Najeriya suyi watsi da kudin albashin da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya saki. Shehu Sani a wata jawabi da saki ranan Alhamis, ya nanata cewa ba zai yiwu ace El-Rufai na amsan albashi kasa da N500,000 a wata ba. Yace :

“ Jama’a kada su yaudaru da albashin da gwamnan Kaduna ya saki ga kafafen yada labarai. “Duk wanda ya yarda da cewa gwamnan jiha zai iya rayuwa da albashi kasa da miliyan 1 kila ya fita hayacin sa ne.”

“Idan ka amince da cewa gwamnan Kaduna yayi gaskiya cewa ya kashe kudin kan na’urar CCTV , ka je Kaduna idan zaka ga na’urar guda daya.” “Idan ka amince da cewa gwamnan jihar Kaduna ya kashe kudinsa akan yan sanda ne, ka tambayeshi da wani kudi ya biya Fulani makiyaya?”

“Idan ka amince da cewa gwamnan jihar Kaduna ya kashe kudinsa akan yan sanda ne, ka tambayeshi da wani kudi ya biya Fulani makiyaya?”

“Najeriya ta asara dukiyoyi da dam aba kawai ga bankunan kasar Swizalanda ba ko kasar Dubai, ba wai cikin gidaje da rufi kawai aka boye suba,; innama dokokin hukumar dabi’a ma ke boyesu.” “Sabanin shugaba Buhari da Osinbajo, babu wani limamin canji da ya shirya bayyana dukiyansa. Kowa na cin karansa ne ba babbaka.” A yau Juma’a, 14 ga watan Afrilu, gwamna Nasir El-Rufai ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a masallacin Juma’an Aso Rock.

vllkyt41j8uk6f5l2.a13d125b

Leave a Reply

%d bloggers like this: