Zamanin Kwankwasiyya Sun Issa? Yan Daba Sun Dawo Kano

Daga Ada’u Bashir

Yau na tsallake rijiya da baya, a wani hari da matasa ‘yan daba ko Area boys da suka kai a kofar Nasarawa da ke Birnin Kano.

Ina zaune a cikin mota na dawo daga kasuwa ina sauka kan Gadar Obasanjo Road, sai kawai na ga mutane na ta gudu ana ta sare-sare ana bin mutane ana kwace musu kudi da jaka.

Kawai sai na ji an sari gilashin motar da adda aka fasa gilashin din ana cewa ku ba mu waya da kudi ko mu kashe ku.

Yara ne kanana dauke da makamai kamar wuka da takobi suna bin mutane da gudu suna musu kwace.

Haka ya sa na koma na bi ta Kofar Mata zuwa gida inda na samu a Kasuwar Rimi ma tuni matasan sun zagaye ta suna yi wa mutane kwace mata da maza.

Babu abinda ya fi ba ni takaici irin yadda suke dukan mata suna cire musu hijabi suna jan su a kasa.

Amma har na kai gida, ban ga koda motar ‘yan sanda na kokarin kai dauki ga al’umma ba.

Abin tambaya anan shine yanzu kenan fada daba ya dawo Kano kenan?

Yanzu a irin wannan halin babu wani mataki da Gwamnati za ta dauka a kan wadannan matasan?

Yunzu Dai Tambaya Ana Shine, A zamanin Kwankwasiyya Danja Wa Issa yayi wannan isgilancin a Birinin Kano?

Kano-State-Governor-Rabiu-Kwankwaso

Leave a Reply

%d bloggers like this: