Mutuwar wuya Phir’auna Ramses na uku yayi inji masanna kimiya

Wasu masanna Kimiya a Kassar Misira sun gano cewa ai Phir’auna Ramses Na uku wata bakar mutuwa yayi inda aka sarsara jikinshi aka yanke mishi wuya kafin ya karasa gidan gaskiya.

Masanan sun gano wannan ne bayan da sukayi aiki da wata Na’ura mai dokan hoton jikin dan Adam akan gawar Phi’aunan.

Tuni daman Makaranta tarihi sun samo takaddun dake nuna cewa anyi wata badakala a zamanin Ramses na Ukun inda wata kishiyar uwar gidansa mai suna Tayi ta nemi ta kashe Ramses da Magajinshi Ramses na Hudu domin itta danta mai suna Pantawaren ya hayye kujerar mulki. Amman ba’a sami wata shaida na chewa wannan rigima ta tabbata ba sai yunzu.

Sarakunan Misira dai masu lakabi da Phir’auna da yawa suna nan a ajiye a gidajen tarihi inda wani irin sallon jan’iza da ak musu yana sa gawawwakin su su jerre dubban shekaru basu yamusheba.

Ga hoton gawar Ramses:

n

n2
Yatsunan Ramses, Masana kimiya sunce sai da aka datsewa sarkin yatsunan kafin a kashe shi, sunce masu mai Jana’iza ne suka dinkesu a jikin gawar sarkin
Leave a Reply

%d bloggers like this: